News
Mun Rufe Asibitocin Bogi Sama Da 100 A Karamar Hukuma Daya — Gwamnatin Kano
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Sama da cibiyoyin kiwon lafiya dari da masana kimiyyar sinadarai ne aka rufe a karamar hukumar Tudunwada da ke jihar Kano, ciki har da asibitin da wani likitan tiyata na jabu da ke ya assasa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Rufewa da kame masu gidajen ya biyo bayan rahotannin mutuwar mata da dama yayin da suka zo haihuwa da kuma marasa lafiya da suka samu nakasu bayan ziyartar da cibiyoyin kiwon lafiyar.
Karamar hukumar, ta damu da irin wannan lamari da aka samu, inda ta kafa kwamitin lafiya karkashin jagorancin wani shugaban al’umma, Abubakar Usman Kareba wanda ya binciki lamarin tare da bankado dimbin cibiyoyin kiwon lafiya na bogi da ke aiki ba bisa ka’ida ba a yankin.
Kareba ya shaidawa manema labarai cewa bayan rufe cibiyoyin kiwon lafiya na jabu, an kama ma’aikatansu.
Ya ce karamar hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakai na shari’a a kan duk wadanda aka kama.
Ina kuma ya kara da cewa, daga ciki wadanda aka kama akwai: mai bada maganin gargajiya dake amsan haihuwar jarirai tare da yin aikin tiyata.
Likitan na bogi, mai suna James Bawa wanda dan jihar Kaduna ne, ya amince cewa yana laifukan da ake tuhumarsa da su, amma ya nemi kwamitin da ya yafe masa tare da alkawarin komawa jiharsa.
Wani Likitan Bogi mai suna Malam Shehu, kuma mai bada magungunan gargajiya, ya yarda cewa ya dade yana aikin tiyata a yankin, kuma yana yi wa marasa lafiya allura da karbar mata masu nakuda.
