Connect with us

News

Yan bindiga sun kai hari gidan wani basarake a Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan sarkin Fadan Ayu, da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da karamin dansa, Sahabi Halidu Ibrahim.

 

Advertisement

Sakataren majalisar sarkin, Jibril Adamu Muhammed, ya shaida wa manema labarai cewa ga dukkan alamu maharan suna harin basaraken ne, saboda kai tsaye da suka shiga gidan dakinsa suka nufa suna harba bindiga.

Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele

‘Yan bindigar sun yi ta harbi amma kuma Allah ya kare basaraken, a don haka ne suka tafi dansa in ji sakataren.

 

Jibril Adamu, ya ce, bayan sun fice daga gidan tare da dan basaraken, sun kira waya inda mahaifiyar yaron ta dauka amma suka ce ba za su yi magana da ita ba sai da mahaifin.

 

Har yanzu dai ana dakon kiran ‘yan bindigar don jin yadda za a yi wajen ceto dan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending