Connect with us

News

Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

 

 

A jamhuriyar Nijar wani jirgin sojin kasar ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka bayan da ya dawo daga wani atisayen soji, lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar sojoji uku.

 

Advertisement

Rundunar sojin Nijar ɗin ta tabbatar da mutuwar sojin ƙasar biyu da na Ukraine ɗaya – waɗanda duka ma’aikatan jirgin ne – a lamarin da ya faru a filin jirgin saman birnin Yamai.

Kane ya ci ƙwallo a wasan Premier na farko bayan hutun Kofin Duniya

BBC ta rawaito cewa  Jirgin ya dawo daga wani atisayen da ya saba yi a lokacin da ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin na Yamai.

 

Kawo yanzu dai hukumomin sojin na Nijar ba su bayyana musabbabin tashin wutar a cikin jirgin ba, sai dai sun ce suna kan gudanar da bincike domin gano musabbabin hakan.

 

A cikin wata sanarwa da ministan tsaron ƙasar ya sanya wa hannu a madadin shugaban ƙasar ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending