News
Ƴan bindiga sun sako mutum 200 da suka sace a Zamfara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun sako sama da mutum 200 bayan sun yi garkuwa da su kwana 20 da suka gabata.
Sai dai kuma masu garkuwar sun kashe kimanin mutum 28 daga cikin 262 da suka yi garkuwar da su.
Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar
Mutanen da aka sako ɗin yawancin su mazauna ƙauyen garin Randa da ke cikin karamar hukumar mulki ta Maru ce.
BBC ta rawaito cewa Sun biya kudi naira miliyan shida daga cikin naira milyan 30 da masu garkuwar suka nema su biya.
Sai dai wadanda aka sako din sun ce ƴan bindigar sun sha alwashin sake sace su idan har ba su biya ragowar miliyan 24 ɗin.
Advertisements
