News
Ƴan Boko Haram sun kashe makiyaya 17 a Borno
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mayakan Boko Haram sun kashe makiyaya 17 tare da sace shanunsu da dama, bayan arrangamar da suka yi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Rfi ya rawaito cewa jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, ‘yan Boko Haram din sun kai farmakin ne tun a ranar Asabar da ta gabata, a daidai lokacin da makiyayan ke gadin dabbobinsu kusa da kauyen Airamne da ke yankin Mafa, inda bayan fafatawa tsakanin bangarorin biyu, 17 daga cikin makiyayan suka rasa rayukansu.
Jami’an sun ce makamai da kuma adadin mayakan na Boko Haram ya zarce na makiyayan sosai.
Daya daga cikin jami’an tsaron sa-kai a Borno, Ibrahim Liman ya ce ‘yan ta’adddan na Boko Haram sun kaddamar da harin na ranar Asabar ne daga dajin Gajiganna, inda suka koma da zama a bisa tilas, bayan da hara-haren mayakan ISWAP da na sojojin Najeriya suka kore su daga dajin Sambisa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
