Connect with us

News

Yan China Na Rububin Tikitin Balaguro Bayan Sassauta Matakan Corona

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

‘yan kasar wadanda suka kasance tamkar saniyar ware daga sauran kasashen duniya na tsawon shekara uku sakamakon tsauraran matakan yaki da coronavirus da gwamnatin kasar ta dauka, yanzu haka suna tururuwar siyan tikitin tafiye-tafiye, gabanin bude iyakokin kasar a wata mai kamawa.

Advertisement

 

Voice of Amurka ta rawaito cewa Hakan kuwa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar ta coronavirus a kasar.

Advertisement

Uwa Ta Aurar Da ’Ya Ba Tare Da Sanin Mahaifinta Ba A Kano

Tsauraran matakan yaki da coronavirus da China ta dauka tun a 2020 – kama daga kulle iyakokin kasar, zuwa yawan sanya matakan kulle – sun tunzura jama’ar kasar a watan jiya nuna babbar adawarsu a fili a karon farko tun bayan da Xi Jingping ya zama shugaban kasar a 2012.

 

Advertisement

 

Yanzu da shugaba Xi ya sauya matsaya kwatsam a game da matakan kulle a kasar, matakan da suka yi mummunan tasiri akan tattalin arzikin kasar, cutar ta coronavirus ta na ci gaba da yaduwa sosai a kasar mai mutane biliyan daya da dubu dari hudu.

Advertisement

 

Sai dai alkaluma hukuma, sun nuna mutun guda ne kawai yam utu sakamakon cutar a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, abin da ya haifar da shakku a tsakanin masana a fannin kiwon lafiya da kuma ‘yan kasar a game da alkaluman.

Advertisement

 

Likitoci sun ce asibitoci sun cika makil da marasa ;afiya, akasarinsu, tsofaffi.

Advertisement

 

Masana kiwon lafiya na kasa da kasa sun yi kiyasin cewa miliyoyin mutane da ke kamuwa da cutar a kowacce rana, za isa a samu mutane miliyan daya da za su mutu sakamakon cutar a badi.

Advertisement

 

 

Advertisement

Daga cikin sassauta matakan, China za ta daina bukatar matafiya dake shiga kasar su killace kansu daga ranar takwas ga watan Janairu.

 

Advertisement

Hukmar shigi-da ficen China ta ce za ta dawo da yiwa ‘yan kasar passport, wadanda suke son yin balaguro zuwa wasu kasashe, sannan za ta dawo da amincewa da bukatun masu son kai ziyara Hong Kong.

 

Advertisement

Darajar Hannayen jarin wasu kamfanoni ta tashi, bayan da Chinan ta sanar da sassauta matakan yaki da cutar ta coronavirus.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending