News
Buhari Zai Kawo Ziyara Kano Domin Ƙaddamar Da Ayyuka – Ganduje.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zo jihar Kano a ranar 30 ga watan Janairu 2023, domin bude wasu muhimman aiyuka da gwamnatin jihar Kano ta gudanar.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis lokacin da yake jawabi yayin bude taron majalisar zartarwar ta jiha wanda ake gudanarwa mako-mako a gidan gwamnatin Kano.
Ganduje Yace akwai ayyuka da yawa da gwamnatin Jihar kano za ta bude a wannan rana, cikinsu akwai babbar gadar sama da kasa, da aka sa Sunan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sannan kuma akwai cibiyar warkar da cutar ciwon kansa, da babbar hedkwatar koyon sana’a.
Akwai hanyoyi a kauyuka kamar daga Janguza zuwa Karaye wadda take kilomita 70 da ta bi ta kananan hukumomi 5.
Gwamna Ganduje yace suna kokari matukar gaske ganin an kammala ayyukan da ake kan yi a wannan lokaci, kasancewar lokaci ya kure amma dai ana duk abinda ya dace ganin an karasa ayyukan da aka dauko.
