News
Yan Sanda Sun Kama Maharan Da Suka Addabi Abuja Da Nasarawa
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Rundunar ’Yan Sandan babban birnin tarayya, ta cafke gungun wasu mutum 10 da ake zargin su da kai hare-hare a Abuja da Jihar Nasarawa.
Da yake gabatar da su a gaban manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Sadiq Abubakar, ya ce an kama wadanda ake zargin a wani otel da ke yankin Masaka, kilomita kadan zuwa Abuja.
An samu bindiga kirar AK-47 guda biyar, sai kwanson harsashi 22 da kuma kananan bindigogi guda uku.
Ragowar abubuwan da aka samu a wajensu sun hada mota kirar Toyota Camry 2000, katin aikin wani dan sanda da kuma janareto guda biyu.
Kazalika, rundunar ta cafke wasu bata-gari hudu da ake zargi da aikata fashi da makami a unguwar Maitama da ke Abuja.
Har wa yau, wadanda ake zargin sun yi wa wani mai sana’ar POS fashin kudi.
An samu karamar bindiga guda uku da harsashi 14, talabijin guda biyu, wayoyin hannu da kuma kayan yari da ake zargin fashin su suka yi.
Rundunar ta kuma gano maboyar wasu masu kai wa ’yan bindiga makamai ne.
