Connect with us

Sports

Aston Villa ta ƙara wa Conte matsin lamba bayan doke Tottenham 2-0

Published

on

yan wasa na karawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta ƙara matsin lamba kan kocin Tottenham Antonio Conte, sakamakon nasarar da ta samu kan ƙungiyar da ci 2-0.

 

Advertisement

Kuskuren da golan Tottenham Hugo Lloris – a wasansa na farko tun bayan dawowa daga gasar Kofin Duniya – ne ya bai wa Emiliano Buendia damar zura ƙwallo kafin Douglas Luiz ya ƙara ta biyu.

Dole Ukraine ta samu tallafi na lokaci mai tsawo – shugaban NATO

Tottenham wacce ke fuskantar matsaloli a baya-bayan nan, ta fice daga huɗun farko a kan teburin Premier League ranar Asabar, a yanzu wasa biyu kawai ta ci daga cikin wasanni bakwai ta ta buga a baya-bayan nan.

 

Magoya bayan ƙungiyar sun yi ta yi wa ‘yan wasan ihu bayan da aka tashi daga karawar, yayin da wasu magoya bayan suka nufi inda shugaban ƙungiyar Daniel Levy ke zaune suna rere waƙoƙin nuna ɓacin rai.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending