News
China na ɓoye ainihin alkaluman cutar korona – WHO
DAGA HASSAN KHALID HAMZA
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa China na ɓoye ainihin tasirin da annobar korona ta yi wa ƙasar – musamman ma alkaluman wadanda suka mutu.
Cire yawancin takunkumai da ƙasar ta yi a watan da ya gabata, ya janyo ƙaruwar mutane masu kamuwa da cutar.
Sai dai China ta daina wallafa alkaluman masu cutar a kowace rana, inda ta sanar da cewa mutum 22 ne kadai suka mutu sakamakon korona tun watan Disamba.
Darektan bayar da agajin gaggawa na hukumar, Dr Michael Ryan, ya ce abin da suke gani a China kan cutar korona ba shi ne ainihin abin da yake faruwa ba musamman idan aka duba wadanda ake kwantar wa a asibiti da ke bukatar kulawar gaggawa da kuma wadanda ke mutuwa sanadin cutar.
Advertisements
