Connect with us

News

Iyaye Da Kungiyar Kungiyar daliban Najeriya Ta Yi Watsi Da Karin Kudin Makaranta

Published

on

DAGA ABDULSAMAD YUSUF

 

Advertisement

Iyaye sun fara kokawa da karin kudin makaranta da wasu jami’oin kasar nan suka yi wasu kuma ke shirin yi, ita kuwa kungiyar daliban jami’oin kasar ta ce bazata sabu ba.

 

Advertisement

Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki zai kasance wata babbar matsala ga daliban da kuma iyayensu.

Makomar tallafin man fetur a Najeriya bayan Yunin 2023

 

Advertisement

Tuni kungiyar ta ce ka kafa wani kwamiti a shiyoyin Najeriya don su zauna da jami’o’in game da yadda za a shawo kan al’amarin.

 

Advertisement

Sanarwar da wasu jami’o’in Najeriya suka fitar cewa daga zangon karatu na gaba a kwana da sanin an kara kudin makaranta, ya yi matukar jefa wasu iyayen da dalibai cikin zukumi da jimami, saboda a cewarsu dama da kyar da jimibin goshi suke biyan kudin makarantar na yanzu.

 

Advertisement

Wani uba ya shaidawa jaridar indaranka cewa ya kadu matuka da ‘yar shi ta kawo mishi takardar batun karin kudin jami’ar.

 

Advertisement

”’Ya ta da ke jami’ar gwamnati da ke Dutse a jihar Jigawa ta kawo min takardar kuma an rubanya kudin har sau biyu, gaskiya gwamnati ya kamata ta saurari kukan mutane, abinci ma na neman gagarar mutane.

 

Advertisement

Kullum su na dabbaka batun yin ilimi, to amma da alama wasu sai dai su hakura da karatun saboda ba su da hanyar biyan kudin karatun.”

 

Advertisement

Suma daliban sun ce sam-sam wannan matakin bai yi dai-dai ba, inda suka kafa kwamitoci a shiyoyin Najeriya don zama tare da samun matsaya da jami’o’in da suka kara kudin ko suke shirin karawa.

 

Advertisement

Kungiyar malaman jami’oin ta ASUU tace da ma ta san za a rina, saboda kudaden gudanarwa da jami’o’in suke karba daga gwamnatin tarayya basa isa.

 

Advertisement

Bayanai na cewa tuni wasu jami’oin suka kara kudin makarantar da fiye da kashi dari, inda karin zai fara aiki a zangon karatu na gaba, sannan wasu da dama ciki har da jami’ar tarayya da ke Dutsen jihar Jigawa suke kan tattauna yadda za su yi kari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending