Sports
Arsenal: An kama mutum biyu da zargin kisan kai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ana tuhumar wasu ‘yan kasar Uganda da laifin kisan kai bayan da aka kashe wani mutum a birnin Kampala bayan da rikici ya barke tsakanin magoya bayan wasu kungiyoyin kwallon kafa na gasar firimiyar Ingila.
Wani kansila ya rasa ransa a sanadiyyar raunukan da ya samu daga wukar da aka daba masa yayin da yake kokarin raba fada tsakanin wasu magoya kungiyoyin kwallon kafa, bayan da kungiyar Arsenal ta sha kaye a hannun Manchester City a wasan da suka buga ranar Juma’a.
CBN Ya Umarci Bankuna Su Fara Ba Da Sabbin Kudi Ta Kan Kanta
Kansilan mai suna Allan Kakumba ya mutu ne jim kadan bayan an kai shi asibiti, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.
Cikin wata sanarwar da suka fiyar, ‘yan sanda sun ce tuni aka kama mutanen da ke da hannu kan kisan kansilan.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
