Connect with us

News

Barazanar Kisa: Kotu Ta Sa A Cafke Shugaban APC Na Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kotu ta ba da umarnin tsare Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya kan zargin barazanar kisa.

 

Advertisement

Babbar Kotun tarayya da ke zama a Kano ce ta sa a tsare, a bincika da kuma gurfanar da Abdullahi Abbas, kan zargin barazanar kisa, tayar da zaune tsaye da kuma kalaman tsana, ga Mahmoud Lamido.

‘Yan sanda sun gurfanar da wani mutum a Kotu da laifin ya ƙara aure.

Mahmoud Lamido ya shaida wa kotun ta bakin lauyansa cewa shugaban jam’iyyar ya kira shi a waya yana barazana ga rayuwar sa da cewa, “Sai na batar da kai.”

Advertisement

 

Akalin koun, Mai Shari’a S.A Amobeda, ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga Fabairun da muke ciki domin ’yan sanda su aiwatar da umarnin.

Advertisement

 

Jam’iyyar NNPP ta bayyana umarnin kotun da cewa babbar nasara ce ga tafiyar dimokuradiyya a Jihar Kano.

Advertisement

 

Kakakin kwamitin yakin neman zaben NNPP na jihar, Sunusi Bature ya yi zargin irin kalaman Abdullahi Abbas na iya kawo yamutsi.

Advertisement

 

A cewarsa, karo na biyu ke nan kotu na umartar Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano ya tsare shugaban APC na jihar.

Advertisement

 

Kawo yanzu dai ba a ji uffan daga bangaren APC ko rundunar ’yan sandan jihar Kano ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending