Connect with us

News

An kai wa gwanan Yobe Mai Mala Buni hari yayin yaƙin neman zaɓe a Gashua

Published

on

Buni

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Gwamnan jihar Yobe da ke arewacin Najeriya Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Gashua da ke ƙaramar hukumar Bade.

Gidan Talabijin na Channels Dubban magoya bayan APC ɗin ne da suka je yakin neman zaɓen suka riƙa yi wa gwamnan ihu suna cewa “ba ma yi, ba ma son Mai Mala Buni”.

An fara rikicin ne lokacin da gwamnan zai miƙa tuta ga ‘yan takarar APC gabanin zaɓen 2023, kawai sai aka fara jifa da dutse da wasu abubuwan na daban.

Sai da aka fitar da Gwamnan daga taron tare da taimakon jami’an tsaro.

Yana yin dai haka ya tilastawa gwamnan da magoya bayansa barin yankin tare da komawa Damaturu ba tare da shiri ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending