News
An Ceto Jaririyar Da Mahaifiyarta Ta Jefa A Masai A Kano
Wata mata ta jefa jariyarta a masai a unguwar Sabon Titi Gidan Kankara da ke Karamar Hukumar Birini a Jihar Kano.
Yayar jaririryar mai shekaru shida ce ta ruga makwabta ta sanar da su abin da mahaifiyar tasu mai larurar kwakwalwa ta aikata, inda suka kira hukumar kwana-kwana don ganin an ceto jaririyar.
Ba za mu daina amfani da tsoffin kudi ba —
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce makwabtan ne suka kira hukumar don ganin an ceto jaririyar kuma an yi nasarar ceto da ranta.
Ya ce bayan samun kiran ne hukumar ta tura tawagar bada agajin gaggawa, kuma “Alhamdulillah an ceto jariryar kuma mun kai wa kakaknta mai suna Abunakar Umar Usman da suke unguwa daya.”
Jami’in ya ce hukumar ta samun labarin cewa shekarun mahaifiar jaririar 25 kuma aurenta ya dade da mutuwa.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
