News
Kotun ƙoli ta ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi
Kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
Atiku ne Ya Tarwatsa Jam’iyyar PDP – Kiyamo
A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.
Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne. ga Yan kasa
Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar
Idan ba,amantaba dai gwamnan babban banki na kasa CBN Godwin da shugaban kasa Muhammadu buhari sune suka bada umarnin da a daina amfani da tsofaffin takardun kudi 500/ 1000
