Connect with us

News

Wasu Yan bindiga sun kashe masarauci a Kano

Published

on

 

 

Advertisement

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Maigarin Kauyen karamar hukumar Rimingado, Alhaji Dahiru Abbas, a yau Lahadi.

Marigayi Abbas shine mahaifin Barista Munir Dahiru, Ciyaman ɗin karamar hukumar Rimingado.

Advertisement

Kotun ƙoli ta ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi

Wata majiya daga iyalin mamacin ta shaida wa manema labarai a Kano cewa maharan da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kai farmaki gidan marigayin da ke kauyen Maigari da sanyin safiyar Lahadi.

Majiyar ta bayyana cewa a lokacin da ƴan bindigar suka zo sun yi wa marigayin raunuka daban-daban kafin daya daga cikinsu ya harbe shi har lahira.

Advertisement

Majiyar ta shaida wa manema labarai cewa za a yi jana’izar sa da karfe 10 na safiyar yau Lahadi a gidan marigayin.

Wakilinmu ya kira kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma wayarsa a kashe.

Advertisement

Ya aika masa da sakon kar-ta-kwana amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu amsa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending