Connect with us

News

INEC ta  Gaza Cimma Burin Ƴan kasa Kamar Yanda suka yi tsammani–Northern States Civil Society Network

Published

on

Sama da mako guda bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, Gamayyar kungiyoyi areawa mai suna Northern States Civil Society Network  ta ce zaɓen ya ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wadda ya lashe zaɓen da adadin ƙuri’u 8,794,726, tazarar ƙuri’a kusan miliyan biyu tsakaninsa da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Advertisement

Kanawa 10 ’Yan Uwan Juna Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kaduna

Jaridar indaranka ta rawaito cewa kungiyar , ta ce ‘yan Najeriya da dama sun fusata game da sakamakon, inda wasu suka riƙa murna kan nasarar da suka samu.

Kungiyar ta ƙara da cewa “A bayyane take cewa tsarin zaɓen Najeriya da aka gudanarar ranar 25 ga watan Fabrairu ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani,”

Advertisement

Kungiyar ta ce “Kamar yadda na sha faɗa a baya gabanin zaɓen, Najeriya ta cimma abubuwa masu yawa a tsawon shekaru sama da 20 da ta yi bayan komawa tafarkin dimoraɗiyya, kuma ci gaban da aka samu a fannin zaɓukan ƙasar na daga cikin nasarorin da ƙasar ta cimma”

“Yan Najeriya sun nuna sadaukarwarsu ga dimokraɗiyya ranar 25 ga watan fabrairu, to sai dai da yawa sun nuna fusata, yayin da wasu da dama suka nuna murna bayan nasarar da suka samu”.

Advertisement

Kungiyar ta kara da  ce ta yi watsi da sakamakon ne saboda INEC ta gaza wallafa sakamakon zaben a shafinta na intanet a manhajar iREV kamar yadda ta yi alƙawari.

Kungiyar tayi allah wadai da sakin alhassan Ado Doguwa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending