News
Ƴan bindiga sun kashe da mace mai ciki a jihar Naija.
Ƴan ta’adda sun hallaka wata mata mai juna biyu na wata shida da wasu mutum huɗu a garin Agwa da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Naija.
Haka kuma ‘yan ta’addar sun sace kusan mutum 50 da raunata wasu a hare-haren da suka kai jiya Talata a yankin ƙaramar hukumar ta Rafi da kuma Wushishi kamar yadda jaridar Vanguard.
Rahotanni sun ce maharan sun riƙa harbin kan mai-uwa-da-wabi a lokacin da suka kai farmakin, sai dai sojoji sun katse musu hanzari inda suka farmake su da hari ta sama.
Duk da cewa sojojin sun kore su to amma ƴan bindigar sun yi awon-gaba da mutum aƙalla 50, yawanci yara da mata kamar yadda bayanai suka nuna.
Al’ummar yankin da abin ya faru na nuna fargaba kan tsaronsu yayin da ake shirin zaɓen gwamna da ƴan majalisar dokokin jiha ranar Asabar.
Kwamishinan tsaro da ayyukan jin-ƙai na jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar da kai harin zuwa lokacin bayyana labarin, ya ce ba su tantance yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
