Sports
Real Madrid ta shiga sahun masu karar Barcelona a kan badakalar cin wasanni
Real Madrid ta ce, ita ma za ta shiga cikin jerin masu karar Barcelona a kan zargin biyan kudi ga alkalan wasa don samun nasara a wasannin La Liga.
Real Madrid wadda ta ce wannan babban zargi ne, ta kira wani taron gaggawa don tattauna batun, inda ta yanke shawarar daukar mataki na shari’a a kan abin da ta kira babban zargi daga masu gabatar da kara.
Madrid ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ta ce za ta shiga lamarin ne don a bi mata kadin cutar da aka yi mata a wasanni.
Ana zargin Barcelona da biyan sama da Yuro miliyan 7 a tsakanin shekara 2001 da 2018 ga wani kamfani mallakinJose Maria Enriquez Negreira, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar alkalan wasa a Spain daga shekarar 1993 zuwa 2018.
A martanin da ta mayar, Barcelona za ta bayyana zargin a matsayin tunanin masu gabatar da kara a matakin farko na bincike, tana mai cewa za ta bada hadin kai a binciken da ake yi.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumuntar Twitter a ranar Lahadi, shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce Barcelona ba ta aikata ba daidai ba.
