Connect with us

Sports

Tsohon Kacin Super Falcons Ismaila Mabo ya rasu

Published

on

Tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya ‘Super Falcons’ Ismaila Mabo ya rasu yana da shekara 79 a duniya.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa tsohon kocin ya rasu ne bayan wata jinya mai tsanani a gidansa da ke birnin Jos da ke jihar Plateau ta tsakiyar ƙasar.

Real Madrid ta shiga sahun masu karar Barcelona a kan badakalar cin wasanni

Marigayin ya jagoranci tawagar Super Falcons zuwa gasar Kofin Duniya ta mata a shekarar 1999 da gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da 2004.

A shekarar 1999 ya jagoranci tawagar wajen samun nasarar da ba ta taɓa samu ba a tarihin wasan Kofin Duniya inda ta kai wasan zagayen kusa da ƙarshe.

A shekarar 1998 ya taimaka wa tawagar matan lashe kofin ƙasashen Afirka ta mata ‘AWCON’, bayan da suka zura ƙwallaye 28 a gasar.

Haka kuma a shekarar 2000 ya jagoranci tawagar wajen kare kofin ƙasashen Afirka ‘AWCON’ da aka yi a Afirka Kudu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending