News
DSS ta tabbatar da maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙo a Najeriya
Hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa DSS ta ce ta shaida wasu jiga-jigai a wata maƙarƙashiya ake kitsawa don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar.
Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wanda wasu ke izawa ba kawai abu ne da ya saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kaucewa.
Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokraɗiyya da kuma zaman lafiyar al’ummar ƙasar.
A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.
Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga ‘yan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.
Ta dai ce masu kitsa makircin, a jerin tarukan da suke yi, suna auna batutuwa da dama a ciki har da yadda za su ɗauki nauyin zanga-zanga maras iyaka a manyan birane ta yadda daga bisani za a ayyana dokar ta-ɓaci.
Wani abin kuma shi ne, su samu umarnin kotu don hana rantsar da sabbin shugabanni da ƴan majalisa a matakin tarayya da jihohi.
Yan adawa a Najeriya sun soki lamirin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara a watan Fabrairun 2023. Sun yi zargin cewa zaɓen yana cike da kura-kurai, kuma an tafka maguɗi, baya ga amfani da tashe-tashen hankula don yin tarnaƙi ga zaɓen 25 ga watan Fabrairu.
Haka zalika, manyan ‘yan adawan da suka yi takara da Bola Ahmed Tinubu kamar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party duk sun shigar da ƙara a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe don ƙalubalantar nasarar Tinubu.
Ita dai Hukumar DSS ta bayyana goyon baya ga ƙudurin Shugaba Buhari na tabbatar da ganin an miƙa mulki ba tare da wani tashin hankali ba, kuma ta ce za ta yi aiki tuƙuru don ganin tabbatar hakan.
Ta kuma ce tana goyon bayan kwamitocin miƙa mulki da shugaban ƙasar ya kafa da kuma waɗanda aka kafa a jihohi.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
DSS ta kuma gargaɗi waɗanda ta kira masu shirin daƙile dimokraɗiyyar Najeriya su janye ƙudurinsu.
Ta kuma buƙaci hukumomi a ɓangaren shari’a da kafofin labarai da ƙungiyoyin farar hula su yi taka tsantsan don kada a yi amfani da su wajen tayar da fitina da ruguza zaman lafiyar ƙasar.
A ranar Talata ma, sai da gwamnatin ƙasar ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa duk da ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da wasu jam’iyyun adawa ke yi, ba za a fasa miƙa mulki hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ba.
Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, ya ce sun shirya tsaf don miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
