News
Dakata! Har yanzu ni ne gwamna – Ganduje ya faɗa wa Abba Gida-Gida
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana

Gwamnatin Kano ta yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Engr Abba Kabir Yusuf ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.
A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zaɓaɓɓen gwamnan a kan su guji janye daga filayen gwamnati.
Gwamnatin Kano ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokaicn da gwamna mai c har yanzu yake kan muli, tamkar riga mallam masallaci ne.
Ta ƙara da cewa kamar yadda yake ƙunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba dazama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.