Connect with us

News

Kungiyar TUC ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan cire tallafin man fetur

Published

on

Ƙungiyar ƙwadogo ta TUC ta gargaɗi gwammatin tarayya da ta guji janye tallafin man fetur a daidai wannan lokaci da ta ce talakawan ƙasar na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.

Ƙungiyar na ganin idan har gwamnatin ta janye tallafin farashin man, to hakan zai ƙara wa jama’ar ƙasar ɗimbin wahalhalu da kuma matsin tattalin arziki.

Abin da kuma ita ƙungiyar ta TUC ke cewa ba za ta amince da shi ba.

A Tattaunawarsa da BBC mai magana da yawun ƙungiyar Kwamared Nuhu Toro ya ce babu yadda za a yi a cire tallafin ba tare da an zauna an tattauna batun cire tallafin tsakanin masu ruwa da tsaki ba.

Ya ce matuƙar aka cire tallafin man to farshinsa zai yi tashin gwauron zaɓi, abin da kuma zai shafi farashin sauran kayayyaki a ƙasar.

Kwamared Toro ya ce cire tallafi ba shi ne mafita wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending