News
An sanya dokar hana fita a wani yankin Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta s’o’i 24 a unguwannin Sabon Garin Nassarawa da Tirkaniya a yankin ƙaramar hukumar Chikun.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne bayan wani rikici na ‘yan sara-suka da ya kaure, da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Sanarwar ta kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar da dokar a unguwar, domin maido da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin abin da ya haddasa hargitsin.
A domin haka ne kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su yi biyayya ga dokar hana fitar, wadda ta fara aiki nan take.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
