News
Jami’an bijilanti sun kama matasa guda 2 da ake zarginsu da satar ƙofofin jama’a watan Ramadana
Jami’an bijilanti a jihar kano reshen Ofishin Adamu Abubakar Fiya fiya,dake unguwa uku yan awaki ta samu nasarar kama wasu matasa guda 2 da ake zarginsu da satar ƙofofin jama’a.
Matasan dai sun hadar da Nura Bala da Yahuza dukkannin su mazauna unguwar Kureƙen sani a Karamar hukumar Kumbotso.
Ramadan na kara nisa hankula kuma sun karkata daga siyayar buda baki zuwa siyayar kayan sallah
Waɗanda ake zargin sun bayyana cewa, ” Ƙofa ce ta wani gida suka cireta kuma ba ta su ba ce, sai dai sun nemi ayi musu afuwa kan laifin da suka aikata.
A nasa Bangaren Kwamandan bijilantin na Unguwa Uku yan Awaki Adamu Abubakar Fiya-fiya ya ce da zarar sun kammala bincike za su miƙa su ga Jami’an yan sanda domin fadada bincike akan su.
“waɗannan barayi ne da rana sai su shiga gidan mutane, ko kuma Kongwaye su ɓalle ƙofofi idan ansa su ɗauka, kuma Allah ya bamu nasara muka kama su a wannan wata na Ramadana.
A karshe ya yi kira ga Jama’a da su dinga sanya idanu akan duk wani motsin da ba su amince dashi ba , su sanar da Jami’an tsaro mafi kusa don kawo daukin gaggawa.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
