Connect with us

News

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kudirin Gyaran Dokar Masarautun Jihar.

Published

on

Majalisar dokokin Kano ta amince da kudirin gyaran dokar masarautu ta jihar Kano ta shekerar 2019.

Majalisar ta amince da gyaran a zaman ta na Talatar nan karkashin kakakinta Hamisu Ibrahim Chidari.

Advertisement

Jami’an bijilanti sun kama matasa guda 2 da ake zarginsu da satar ƙofofin jama’a watan Ramadana 

Gyaran dai ya kunshi rage mambobin majalisar zartaswa ta sarakunan jihar Kano zuwa mutane goma sha bakwai maimakon mutane 25.

Haka kuma gyaran ya bayar da damar samar da gidajen da zasu iya gadar sarki koda Allah yayi wani sarki ya rasuwa daga cikin sarakunan Kano.

Advertisement

A wani cigaban kuma majalisar dokokin ta amince da sabon taken jihar Kano wanda za a rinka amfani dashi a guraren taruka a fadin jihar nan.

Gwamnatin Kano da jami’ar Bayero ne dai suka samar da taken na jihar Kano.

Advertisement

Majalisar ta kuma karbi takardar daga gwamnan Kano dake neman sahalewa domin samar da hukumar da zata rinka kula da tituna a yankunan karkara.

Haka kuma  majalisar dokokin ta Kano ta kuma karbi takarda daga gwamnan Kano dake neman majalisar ta amince da Balarabe Hassan Karaye a matsayin kwamishina a hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC).

Advertisement

Majalisar ta kuma dage zaman ta zuwa Larabar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending