Connect with us

News

Sabon zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilan  ya rasu

Published

on

 

 

Advertisement

 

Wani sabon zababben dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar ya rasu ranar Juma’a 21 ga watan Afirilu 2023, da daddare.

Advertisement

 

Ismaila Maihanci wanda aka zaba domin wakiltar mazabar Jalingo da Yorro da Zing a majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Taraba ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Abuja.

Advertisement

Wasu ne za su cinye kudin rage radadin tallafin mai ba talakawa ba – Sanata Ndume

Wani makusancin zababben dan majalisar ne ya tabbatar wa BBC rasuwar inda ya ce mutuwar ta girgiza iyalansa da kuma makusanta.

 

Advertisement

Ya kara da cewa wannan babban rashi ne ga al’ummar jihar Taraba.

 

Advertisement

Ba don rasuwarsa ba da zai kasance karon farko da marigayin, dan jam’iyyar PDP zai je majalisa bayan kayar da wanda ke kan kujerar, Kasimu Bello Maigari na jam’iyyar APC.

 

Advertisement

Ismaila wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar na majalisar tarayya a watan Fabarairu ya kasance daya daga cikin fitattun matasan ‘yan siyasa a jihar Taraba.

 

Advertisement

An sa ran yin jana’izarsa a ranar Asabar din nan 22 ga watan Afirilu, a Abuja.

 

Advertisement

An haifi marigayin mai shekara 37, a watan Oktoban shekara ta 1986.

 

Advertisement

Mamacin ya yi fice ne kasancewarsa dan kasuwa kuma matashin dan siyasa a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending