Connect with us

News

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga mutumin da ya kashe maƙwafcinsa 

Published

on

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin kashe maƙwafcinsa

 

Advertisement

Wata babbar kotun jihar Ekiti dake zama a birnin Ado Ekiti, ta yanke wa wani mutum mai suna Isma’ila Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin kashe maƙwafcinsa mai suna Kareem Adu kan saɓanin dake tsakanin game da maganar babur.

 

Advertisement

Adamawa: Binani ta janye ƙarar da ta shigar a kan INEC

An dai gurfanar da Ojo ne gaban kotun inda kuma kotun ta same shi da laifin kashe maƙwafcinsa a ranar 13 ga watan Mayu shekarar 2018.

Alkalin kotun mai shari’a Olusegun Ogunyemi, ya ce, ya gamsu cewa wanda ake tuhumar shine ya kashe maƙwafcinsa nasa ta hanyar shaƙe masa wuya da makogwaro har sai da ya rasa ransa. Saboda haka kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Tun farko ɗan sanda mai shigar da ƙara Sifeta Tunde Arowosola ya shaidawa kotun cewa, wata mata mai suna Agnes Adu ita ce ta zo Ofishin yan sanda tayi ƙorafin cewa wani mutum ya kashe mijinta sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan ikon mallakar babur, sakamakon haka ne a cewar sa yan sanda ba tare da bata lokaci ba suka kama wanda ake zargin suka gurfanar da shi gaban kuliya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending