Fitacciyar manhajar sadarwar nan ta WhatsApp ta saki wata sabuwar fasaha wadda za ta bai wa mutum damar amfani da lamba ɗaya ya buɗe whatsaApp a kan wayoyi daban-daban.
Bayan samar da wannan fasaha, yanzu za a iya amfani da lamba ɗaya a buɗe WhatsApp kan wayoyi har guda huɗu.
Kotu ta yanke hukuncin kisa ga mutumin da ya kashe maƙwafcinsa
Ta yadda za a iya aika saƙo da hoto da bidiyo, kuma zai kasance babu wanda ya isa ya datse shi, a kan duka wayoyin.
Idan wayar da lambar WhatsApp ɗin take ta daɗe ba ta aiki, to sauran WhatsApp ɗin duka za su tsaya su daina aiki.
Da wannan sabuwar fasahar, yanzu yadda shiga, da yadda ake fita WhatsApp zai sauya tsari.
