News
NECO Ta Canja Ranar Jarabawar NCEE Ta Bana 2023
Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta dage jarabawar gama gari ta kasa (NCEE) ta shekarar 2023 daga ranar Asabar 29 ga watan Afrilu 2023 zuwa Asabar 3 ga watan Yuni 2023.
Hukumar NECO ce ke gudanar da jarrabawar gama gari ta kasa duk shekara domin daukar dalibai a kwalejojin hadin kan tarayya da ke fadin kasar nan.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Azeez Sani, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa an sake jadawalin jarabawar ne domin baiwa Jihohin da ke da karancin rijistar damar yin rijistar wadanda za su yi jarrabawar,Tribune Online ta rawaito.
“Don haka an umurci dukkan ‘yan takara, iyaye, masu gadi, makarantu da masu ruwa da tsaki da su lura da sabuwar ranar da za a yi jarabawar.
“Za a ci gaba da yin rijistar ‘yan takara har zuwa ranar da za a gudanar da jarrabawar,” in ji Sani.
