Connect with us

News

Kungiyar Dalibai ta kasa NANS Zata Yiwa Gwamnati Bore Kan Karin Kudin Makaranta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi barazanar cewa za ta tsayar da dukkanin wasu ayyuka a fadin kasar nan, idan har gwamnatin tarayya ba ta janye karin kudaden karatu na manyan makarantu ba.

Advertisement

 

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Usman Barambu shi ne ya yi wannan barazanar a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali da ke jihar Bauchi.

Ranar Litinin Mai Zuwa Za’a Fara Rubuta Jarabawar WAEC

Ya ce karin kudin makaranta ya yi illa ga yawancin daliban da ke makarantun gaba da sakandare.

 

Shugaban kungiyar ta NANS ya yi gargadin cewa idan har Gwamnatin Tarayya ba ta gaggauta janye matakin ba, kungiyar za ta zaburar da daukacin daliban manyan makarantun kasar nan domin gurgunta duk wasu harkokin gudanar da aiyukan gwamnati a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending