News
Allah Ya yi wa daya daga cikin limaman Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina, rasuwa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Allah Ya yi wa Sheikh Muhammad Khaleel Al-Qari, daya daga cikin limaman Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina, rasuwa.
Kafin wayewar garin Litinin Allah Ya yi wa malamin rasuwa, kamar yadda Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami da na Madina ta sanar ta shafinta.
Dangote Ya Bayyana Ranar Da Zai Kaddamar Da Kamfanin Matatan Mai.
Ta bayyana cewa za a gudanar da Sallar Jana’izar malamin da Magriba, idan Allah Ya kai mu.
Sheikh Muhammad Khaleel Al-Qari yana daga cikin limamai baki da ke jagoracin Sallar Tarawih a masallacin, da ke karbar bakuncin miliyoyin masu ziyara a duk shekara.
-
Opinion3 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
