News
Rundunar Yan sanda Sun Kama Mutumin Da Yayi Yunkurin Bankawa Masallaci Wuta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
‘Yan sanda sun kama wani mutum da ya yi yunkurin cinnawa wani masallaci wuta a birnin Dresden na Jamus da yammacin jiya Talata.
Jaridar post ta ruwaito cewa Mutumin ya zuzzuba fetur a kewayen wani masallaci tare da kokarin cinnawa ginin wuta, in ji kakakin ‘yan sandan.
Kungiyar ECOWAS ta sake yin kiran a murkushe ta’addancin da ke karuwa a tsakiyar Sahel
Shaidu gani da ido, sun kira lambar hukumar bayar da agajin gaggawa bayan da suka ga mutumin yana zuba mai a harabar masallacin, wanda a lokacin ya shiga hannu
An kama mutumin mai shekaru 34, kuma yana karkashin binciken ‘yan sanda kan yunkurin tada kayar baya.
Ko da yake da farko ba a san dalilinsa ba, amma an ce wanda ake zargin ya kona wani kwafin Alkur’ani mai girma a wani masallaci a watan Afrilun shekarar nan.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
