Connect with us

News

Uwa ta rasa ranta a kokarin raba faɗa tsakanin ‘ya’yanta a Abuja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wata mata mai suna Zainab Ibrahim ta rasa ranta a kokarin raba fada tsakanin ‘ya’yanta maza biyu, Inusa da Usman.

Advertisement

Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da ya hadasu, Inusa, bayanai na nuna cewa ya yi amfani da wuka wajen soka mahaifiyar a bisa kuskure a hannunta na dama.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kpaduma da ke Asokoro a Abuja.

Advertisement

Akwai Yiwuwar Ambaliyar Ruwa A Wasu Sassan Arewacin Najeriya

Wani mazauni unguwar Saliu Shehu ya ce an gagauta kai Zainab asibiti amma daga baya sai rai ya yi halinsa.

A lokacin da aka tuntube shi, kakakin ‘yansanda Abuja, Josephine Adeh, ya ce Inusa ya tsere amma ana bincike kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending