Connect with us

News

wata mata a kano Ta Yi Garkuwa Da Dan Kaninta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Dubun wata mata mai shekaru 45 ta cika bayan da ta yi garkuwa da dan kaninta da nufin karbar kudin fansa Naira miliyan 20 daga hannun mahaifinsa.

Matar wadda ke zaune a unguwar Gwammaja a Karamar Hukumar Dala ta  Jihar Kano ta shiga hannu ne tare wasu maza uku da ta hada baki da su wajen sace yaron mai shekara shida a duniya.

Advertisement

Uwa ta rasa ranta a kokarin raba faɗa tsakanin ‘ya’yanta a Abuja

DAILY trust ta gano cewa a watan Afrilu ne iyayen yaron suka kai rahoto ofishin ’yab sanda cewa ya nace.

Daga baya wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kira mahaifinsa suna neman kudin fansa Naira miliyan 20, amma daga baya suka daidaita a kan Naira miliyan biyar.

Advertisement

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel, ya ce daga baya, ’yan sanda suka ceto yaronbba tare da wani abu ya same shi ba.

Ita kuma yayar mahaifin nasa aka cafke ta tare da sauran mutum ukun da ta hada baki da su.

Advertisement

Da take bayani, matar ta bayyana cewa, “Maihaifinsa kaninta ne, kuma na yi ne domin in samu wasu kudade, amma ko miliyan daya ban samu daga cikin miliyan biyar da din ba.

“Bayan sun karbo kudin ne aka kama ni; Na yi da-na-sanin abin da na yi.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending