Connect with us

News

Wannan ƙabilar dai sun yi ƙaurin suna a Duniya saboda wannan al’ada tasu ta sanya faranti a leɓe.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Yayin da budurwa ta kai kimanin shekaru Goma Sha Biyar, sai a samu wata matar a cikin gari ta zo a kawo mata wannan yarinyar, in da ita kuma aikin ta shi ne, za ta tsaga leɓen da aska sai kuma a saka ƙaramin sanda ya tokare tsagar domin kar ta haɗe.

A hankali ana kula da wajen har ta kai ga an fara sanya ƙaramin faranti wadda aka yi masa zanen ado a jiki. A haka dai za a yi ta sauya farantan har iya girman farantin da ake so faɗin leɓen ya kai.

Advertisement

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Harbe Ɗan Uwansu A Kano

Sukan cire farantin yayin da mazajensu suka fita domin noma da kiwo, ko Su, ko farauta, amma da zarar maraice ta yi sun laƙanci lokacin dawowarsu, sukan mayar domin nuna girmamawa ga mazanjen su.

A wurin ƴan ƙabilar Mursi, duk mace da ba ta da wannan tsagar leɓen mai faranti, to raguwa ce, ma’ana; Malalaciya.

Advertisement

Sannan kuma in an tashi yin aurenta, saurayin ba zai biya sadakin kirki ba. A taƙaice dai ba ta da daraja a wurin mai auren nata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending