Connect with us

News

NCC: Yau Za A Koma Amfani Da Lambobin Loda Kati Da Data Na Bai-Daya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta sanya domin komawa amfani da gajerun lambobin sanya kati da data na bai-daya a Najeriya.

Umarnin hakan da ke kunshe a cikin sanarwar da hukumar NCC ta fitar a watan Maris ya nuna daga yanzu, babu bambanci a gajerun lambobin sanya kati ko data dangoginsu a layukan duk kamfanonin sadarwa a Najeriya.

Wannan ƙabilar dai sun yi ƙaurin suna a Duniya saboda wannan al’ada tasu ta sanya faranti a leɓe.

Ta bayyana cewa daga yanzu lambar loda katin waya ita ce *311*lambar katin sannan#.

Ga jerin gajerun lambobin da amfaninsu:

Advertisement

300 – Kiran cibiyar hulda da jama’a.

301 – Tura sakon murya.

302 – Bude sakon murya.

303 – Karbar rance.

305 – Ficewa daga tsari.

310 – Duba kati.

Advertisement

311 – Sanya kati.

312 – Tsarin data.

321 – Tura wa wasu.

323 – Duba data.

966 – Hada layi da katin dan kasa

2442 – Dakatar da sakonnin talla.

Advertisement

3232 – Sauya network.

Sanarwar da hukumar NCC ta fitar a ranar 13 ga watan Maris ta ce lambobin bai-dayan za su saukaka wa masu amfani da waya a Najeriya wahalar da a baya suke yi na rike lambobin kowane kamfanin sadarwa da suke amfani da layinsa.

 

Ta ce ta ba da wa’adin 17 ga watan Mayu ne domin kamfanonin sadarwa su samu sauye-sauyen da suka kamata.

 

 

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending