Sports
Real Madrid ta soke kwantiragin Eden Hazard daga kungiyar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Real Madrid ta soke kwantiragin Eden Hazard daga kungiyar,kamar yadda jaridar Daily Post ta rawaito.
Bangarorin biyu sun amince da kulla yarjejeniyar a ranar Asabar.
A wata sanarwa da Real Madrid ta wallafa a shafinta na yanar gizo ta ce “Real Madrid CF da Eden Hazard sun cimma yarjejeniya ta yadda za a sako dan wasan daga kungiyar har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023.”
Firaministan kasar Indiya ya ci alwashin hukunta masu sakaci a haɗarin jiragen ƙasa
“Real Madrid na son bayyana soyayyarta ga Eden Hazard kuma tana yi masa fatan alheri da dukkan iyalansa a wannan sabon matakin.”
Hazard dai ya sha fama da matsananciyar wahala a Bernabeu tun lokacin da ya koma kungiyar daga Chelsea a shekarar 2019, kuma ya kasa cika abin da ake tsammani daga lokacin da ya sanya hannu a kwantiragin.
A cikin shekaru hudu da ya yi a Sipaniya, dan kasar Belgium ya lashe Kofin Turai, Kofin Duniya na Club World Cup, Super Cup na Turai, Gasar Lig guda biyu, Copa del Rey daya da kuma Super Cup na Spaniya guda biyu.
