News
INEC Ta Amince Da Sunayen ‘Yan Takarar Gwamna A Jahohin Bayelsa, Kogi Da Imo.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADIN
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta amince da jerin sunayen ‘yan takara na karshe na zaben gwamna da za’a gudanar a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Kwamishinan yada labarai na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Festus Okoye ne , a wata sanarwa da ya fitar ya ce amincewar ta yi daidai da tanadin dokar zabe da ke bukatar a fitar da jerin sunayen, kwanaki 150 kafin ranar zabe.
Majalisa ta bukaci Tinubu ya hukunta masu hannu a damfarar Nigerian Air
Okoye ya ce jerin sunayen na karshe da hukumar ta wallafa a shafinta na Internet ya nuna jam’iyyun siyasa 18 ne suka tsayar da ‘yan takara a Kogi sai 17 a Imo da 16 a Bayelsa.
Ya kara da cewa za a fara yakin neman zaben a hukumance a ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, don haka ya shawarci jam’iyyun siyasa da su kauracewa rigingimu su gudanar da harkokinsu cikin lumana.
