Politics
Al’umma a yawaita addu’a don samun zaman lafiya….Muslim Yunus Abdullahi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar kansila a mazabar unguwar tudun wada Ward dake karamar hukumar Gwarzo, Muslim Yunus Abdullahi yayi kira ga al’umma dasu cigaba da yiwa kasar nan addu’a don samun zaman lafiya mai dorewa.
Ya Kara da cewa Kada a gajiya wajen yin addu’a don samun zaman lafiya da Kuma samun shugabanci nagari.
Muslim Yunus wanda ke takara karkashin jam’iyar NNPP yayi wannan kirane a sakon barka da sallah wanda mai taimakamasa na musamman kan kafofin yada labarai muhammad muhammad ZAHRADDIN ya fitar a ranar talata.
Iyayen Yara sun fara kokawa akan Karin kudin da Jami’ar Bayero da ke Kano ta yi.
Ya ce za samu saukin matsalar tsaron da kasar nan take ciki ne kawai ta hanyar addu’a tare da mika lamura ga Allah madaukakin sarki.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Gwarzo da kewayi su futu domin kada kuri’un su a zaben 2023 dake tafe na Shugaban kanan hukumomi da Kuma na kansiloli
Muslim Yunus ya kuma ce ba zai baiwa al’ummar unguwar tudun wada , kunya ba matukar suka zabe shi amatsayin kansila su
Ya kuma yi fatan al’ummar jihar Kano zasu cigaba da shagulgulan sallah lafiya.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
