Connect with us

Politics

Ina Jiran Lokaci Domin Allah Shine Mai Bada Mulki —Ibrahim tijjini bala

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Dan takarar kansila a mazabar yalwa Ward dake karamar hukumar Dala , IBRAHIM Tijjini bala yace Ina jiran lokacine domin Allah Shine mai bada mulki.

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa, yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe na shugabanci kananan hukumomi da Kuma kansiloli na 2023, ƴan takara da dama na jam’iyar NNPP da kuma APC dama PDP a karamar hukumar dala na nuna buƙatar su ta tsayawa domin wakilci na al’ummar mazabar yalwa.

Yan daba sun kashe wani Dan kasuwa  har lahira a Kano

Sai dai kuma, wannan jarida ta gano cewa kawo yanzu, ba a ga wata alama da ta nuna cewa dan takarar bazaiyi nassara ba a wannan lokacin
Amma, a wani sakon barka da sallah dan jiyo IBRAHIM na cewa ita magana ta siyasa ko muƙami, abu ne da Allah ne Ya ke yi.
A cewar IBRAHIM, ban da Allah, babu wanda zai iya baiwa wani muƙami, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya kaɗai kugen siyasa da wuri ya san Allah ne ke yi, haka-zalika wanda ya jira sai nan gaba shima ya san Allah ne ke yi.

Advertisement

“Ita maganar siyasa ko maganar muƙami, kowa dai ya san Allah ne Ya ke yi. Banda Allah ba bu mai yi kuma a kwai lokaci.
“Wanda ya buga kugen sa da wuri ya sani, wanda kuma ya bari ya jira lokacin Allah, shima kuma ya sani.
Haka Kuma IBRAHIM ya kuma ce ba zai baiwa al’ummar unguwar yalwa kunya ba matukar suka zabe shi amatsayin kansila su
Ya kuma yi fatan al’ummar jihar Kano zasu cigaba da shagulgulan sallah lafiya.

“Mu na jiran lokacin Allah, Allah kuma Shi ne mai yi,” in ji IBRAHIM .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending