Connect with us

Politics

Kwankwaso: Mutane Sun So Na Rushe Musu Gida Lokacin Ina Gwamna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran sansanin siyasar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana irin kwarewar da ya samu a matsayin gwamna a jihar Kano.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa Ya bayyana wannan kwarewar ne a wata hira da gidan Rediyan Faransa International (RFI).

Advertisement

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce ba zai tsaya takara ba a zaben 2024

Ya kuma yi tsokaci kan zarge-zargen da ake yi masa na cewa shi ne ke juya gwamnan jihar, inda ya bayyana wadanda ke fadin haka a matsayin tsofaffin ‘yan kungiyar Kwankwasiyya.

Da aka tambaye shi game da shigarsa cikin harkokin gwamnati mai ci musamman kan aikin rusau da ake yi,

Advertisement

Sai ya ce, “Duk wannan bata lokacinku kuke. Abin da mutane ke so shi ne su ga aiki a kasa. Mu tawaga ce. Duk abun ƙiyayya ce kawai daga yan adawarmu daga cikin waɗanda suka fice zuwa ga tsagin masu hamayya kuma suka bata.mu. Ganduje ya kammala kuma yayi nasara.

“Wannan rusau da aka yi mana gyara ne kuma abu ne da muke cewa tun 2019 duk gwamnan da ya gina makarantu, masallatai ko Badala ba za mu bari ba.

Advertisement

“Idan ka duba, kawai a ba da wuraren da aka taɓa. Babu wata manufa a duniya da ta ce ku rusa jami’a ku gina shaguna.”

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Da yake magana game da kuma raba filaye tare da Badala ga mutane a lokacin da yake Gwamnan Jihar, ya ce.

Advertisement

“A shekaru takwas da na yi mulki a matsayin gwamna, ban ba kowa kafa daya daga makaranta ba daga firamare har zuwa sakandare.

“Lokacin da muke samar da shimfidar filaye a Kano, wurare irin su Kwankwasiyya, Danladi Nasidi da sauran su, mun biya diyya har ninki goma.

Advertisement

“A lokacin mutane suna fatan mu rushe gidajensu don mu biya su diyya“.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending