Connect with us

News

Na Rabu Da Budurwata Saboda Rashin Bin Ƙa’idojin Rubutu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wani mai amfani da shafin sada zumuntar Facebook ya yanke shawarar kawo karshen alaƙarsa da wata sabuwar budurwarsa da ya haɗu da ita ta yanar gizo saboda rashin kwarewar rubutun da bata da shi.

Ya bayyana bacin ransa ne a wani rubutu da ya wallafa a Facebook wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta.

Advertisement

A cikin sakonsa, ya rubuta cewa

“Mun kwashe kwana uku muna hira amma kwata-kwata bata yi amfani da waƙafi ko guda ɗaya ba, ko ma alamar tambaya! Sai kawai ta ce “Ka ci abinci” menene haka? Tambaya kike ko labari kike bani!? Kar ma fa ace ta yi amfani da manyan ƙa’idojin rubuta kamar su baka-biyu, alamar motsin rai da makamantansu. Kuma haka take rubuta “lagos” da jihohin Najeriya da ƙananan baƙi hatta Abuja “abuja” take rubutawa.

Advertisement

Kotu Ta Daure Wani Mutum Shekaru 235 gidan yari a Bayan Samunsa Da Laifi

Itodo, wanda malami makaranta ne, ya ce ba zai iya jure wa hawan ƙawarar da budurwarsa ke yiwa nahawu ba a rubutunta.

Rubutun nasa ya jawo dubban masu martani da tsokaci daga sauran masu amfani da shafin na Facebook.

Advertisement

Wasu daga cikinsu sun goyi bayan shawarar da ya yanke na rubutawa da ita, sunw kuma darajanta ƙa’idojin rubutu a cikin zamantakewar soyayyarsu.

Wasu kuma sun ce yin rubutu da dai-daito ba wani abu ba ne mai girma, don haka ya kamata ya mayar da hankali kan wasu al’amura na halin budurwar sa, ya kawar da kai kan rubutunta.

Advertisement

Wasu kuma sun ce wannan ai ba komai ba ne a ƙasa Najeriya, mutane na da matsalolin da za su iya magance su da yawa ba wannan ba.

Sun ce ƙa’idojin rubutu bai dace da tattaunawar yau da kullun ba kuma mutane za su iya fahimtar juna ba tare da shi ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending