Connect with us

News

Hukumomi Na Zargin Bangarori Masu Zaman Kansu A Harkar Tsaro Da Kawo Cikas Wajen Dakile Yaduwar Kananan Makamai A kasar nan

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Cibiyar dake kula da kanana makamai ta nuna damuwar ta kan yarda ake samun karuwar cibiyoyin tsaro masu zaman kansu dake bayyana kawunan su amatsayin wadanda gamnati ta sahalewa kula amfani da makamai a kasarnan, musamman ma a yankin Arewa ta tsakiya.

Jami’in tuntuba na yankin Major Janaral Hamza Bature mai ritaya ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manma labarai a shalkwatar cibiyar dake Minna.

Advertisement

Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Fitar Da Sabon Wa’adi Ga Gwamnatin Najeriya

Yace bayanan da cibiyar ta gano a kwanan nan sun bayyana cewa irin wadannan kungiyoyi sun kai ga yaudarar al’umma jihar Kogi da yi musu alkawarin basu ayyukan yi don taimakawa wajen kwace kananan makamai.

Bature ya koka kan cewa ayyukan irin wadannan kungiyoyi da basu da sahalewar gwamnati, suna kawo tsaiko ga ayyukan cibiyar na tabbatar da ganin Najeriya ta kasance kasar da ba’a yin amfani da kananan makamai barkatai, yayin da kuma yace hakan zai iya bata sunan cibiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending