News
Mai Juna Biyu Ta Gamu Da Ajalinta Saboda Yajin Aikin Likitoci A Jihar Nasarawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata mata mai matsakaicin shekaru a jiya rahotanni sun bayyana cewa ta rasa ranta a jihar Nasarawa saboda rashin likita da zai duba ta.
Hakan ya biyo bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da likitoci masu neman kwarewa reshen asibitin kwararru na Dalhatu da ke Lafiya suka gudanar.
Matar mai juna biyu wadda ba a bayyana sunanta ba a asibitin kwararru na Dalhatu da ke Lafiya, rahotanni sunce an tsara za’ayi ma ta tiyata.
Sai dai aikin bai samu ba saboda yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Ta rasu ne a lokacin da take jiran likitoci su kula da ita.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
