Connect with us

News

Ka yi nazarin akan manufofinmu na ilimi kafin yin suka, Kiru ya mayar da martani akan sabon kwamishinan ilimi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Gwamnatin da ta shude a jihar Kano ta ce ya kamata gwamnatin New Nigeria People’s Party (NNPP) ta yi nazari a kan manufofinta kan ilimi kyauta kafin ta yi suka a kanta.
Tsohon kwamishinan ilimi a gwamnatin da ta shude Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani jawabi da ya yiwa sabon kwamishinan ilimi Honarabul Umar Haruna Doguwa, inda aka ambato shi yana cewa gwamnatin da ta shude batayi abun karki ba a fannin ilimi ba.

BREAKING NEWS:Hukumar DSS ta gurfanar da Emefiele a Kotu

Yana mai cewa Tsarin Ilimi na wajibi na firamare da na Sakandare da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bari a baya na da kura-kurai.
Ya shawarci Doguwa da ya sassauta, ya bi ta ya fahimci manufofin da masana ilimi, masu kula da manufofi, masu fasaha, masu rajin ci gaba, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran su suka samar da tsaran kafin fara suka.

Advertisement

Kiru ya kuma yi kira gare shi da ya zage damtse wajen samar da muhimman bukatun makarantun da ke karkashin ma’aikatar a maimakon mayar da shi jami’in gwamnati mai ciwon baki.
Ya kara da cewa “Na yi Allah-wadai da kakkausar murya, kalaman da abokina kuma dan’uwana ya yi dangane da manufofin ilimi da muka bari a baya cikin kasa da watanni biyu a kan mulki.

Tsohon kwamishinan ya ci gaba da cewa, abin takaici ne matuka yadda sabon kwamishinan yake amfani da dalilai a wajan siyasa.

Advertisement

Na lura cewa wannan yunƙurin da gwamnatin NNPP ta yi na mayar da fannin ilimi a siyasance, wata manufa ce ta ganganci na lalata gagarumin nasarorin da Ganduje ya samu tsakanin 2015 zuwa 2023.

Kiru ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin NNPP ta dakatar da zage-zage, ta kuma yi abin da ya dace ta hanyar inganta nasarorin da gwamnatin Ganduje ta samu a cikin shekaru takwas da suka gabata.

Advertisement

Ya ce yunkurin da Ganduje ya yi na ganin an shawo kan lamarin cikin watanni shida da ya yi yana mulki ya sa babu wanda ke cikin shakku kan muradinsa na kawo sauyi ga tsarin da ba a taba gani ba.
Kiru ya yi nuni da gamsuwa da cewa ayyukan da tsohuwar gwamnatin ta yi ta samar da sakamakon da ake so.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending