News
Allah yayi wa Matar Dahiru Mangal Rasuwa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Allah Ya yi wa matar hamshakin attajirin dan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal rasuwa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Hajiya Aisha Mangal ta rasu ne da Yammacin wannan Asabar.
Shin Ko Kun San Nawa Ne Farashin Motocin Da Za A Siya Ma Yan Majalisa?
Bayanai sun ce ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja inda ta yi ’yar gajeruwar rashin lafiya.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoto babu wani bayani dangane da shirye-shiryen jana’izarta.
Advertisements
