News
Rashin fitilun filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya sa an juya da fasinjoji zuwa Legas.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rashin fitilun filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya sa an juya da fasinjoji zuwa Legas.
Fasinjojin jirgin Airpeace da ya taso daga Abuja a yammacin Asabar sun shaidawa Freedom Radio cewar bayan da jirgin ya iso Kano sai aka ce su dakata har sai an gyara matattun fitilun filin jirgin.
Yadda ‘yan Tiktok ke son hada kai da rundunar ‘yan sanda don kawo gyara a Kano
Bayan tsahon mintuna 30 suna shawagi a sama fitilun basu kama ba sai direban jirgin ya koma dasu Abuja, can kuma da suka je rashin kyawun yanayi yasa basu iya sauka ba dole suka wuce suka sauka a Legas.
Muna tafe da ƙarin bayani a Labaran An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safe idan Allah ya kaimu.
Advertisements
