News
Shin da gaske ne gwamnatin Kano ta soki Shugaba Tinubu?
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke cewa ta soki shugaban kasar Bola Tinubu a kan tsarin raba N500bn ga kananan masana’antu a fadin kasar.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Asabar, ta “nesanta” mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo da sukar shugaban kasar game da yadda aka fifita wani bangare na kasar wajen rabon kudin.
Rashin fitilun filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya sa an juya da fasinjoji zuwa Legas.
Sanarwar, wadda kakakin mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shu’abu ya fitar ta ce Aminu Gwarzo ya yi tsokaci ne game da wani labari da ya gani inda Sanata Ali Ndume, dan majalisar dattawan kasar, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka bai wa wani bangare na kasar kaso mafi tsoka na kudin.
“Babu wani wuri a jawabin mataimakin gwamna da ya ambaci sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji shi, yana mai karawa da cewa an yi tsarin raba kudin ne tun kafin “Shugaba Tinubu ya hau kan mulki.”
Wannan batu dai ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a arewacin Nijeriya inda wasu ke gani bai kamata a ware wa kudancin kasar kaso mafi tsoka a bashin da bankin kula da kananan masana’antu yake bai wa ‘yan kasar ba.
